Ministar Burtaniya Vicky Ford za ta ziyarci Najeriya  domin tallafa wa ‘yan kasuwa da kuma inganta hadin gwiwar tattalin arziki

Ministar Burtaniya a Afirka, Latin Amurka da Caribbean, Vicky Ford za ta ziyarci Najeriya a wannan makon a ziyarar ta ta farko a kasar. Sanarwar da babbar hukumar Biritaniya a Najeriya ta fitar ta ce, ziyarar ta biyo bayan tattaunawar tsaro da kasashen Birtaniya da Najeriya suka yi a birnin Landan a farkon wannan wata, inda Birtaniya da Najeriya suka amince da karfafa hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da hadin gwiwar soji, da yaki da ta’addanci da aikin ‘yan sanda na farar hula tare da kare hakkin bil’adama da kuma sanin muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa. 

Sanarwat ta ce ziyarar za ta ci gaba da kokarin da kasashen biyu ke yi na bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu da kuma karfafa dangantakar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki.

Yayin da take Najeriya, minista Vicky Ford, za ta gana da gwamnatin tarayyar Najeriya, gwamnonin jihohi da kuma shugabannin addinai da kungiyoyin farar hula da ‘yan kasuwa. Ministan ,na fatan ayyana miliyoyin fam – famai na Burtaniya na jati gami da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu. 

Ta kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da cin hanci da rashawa, wanda zai kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Birtaniya da Najeriya a wannan fanni. Har ila yau, ministar za ta inganta kokarin ilmantar da ‘yan mata da  karfafawa mata da kuma kawo karshen cin zarafin matan  tare kuma da magance bukatun jin kai a Arewa maso Gabas .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *