An bayyana cewa, Najeriya ta yi hasarar mutane dubu biyu da talatin da takwas, a cikin shekaru Hamsin da ukku da suka gabata,sakamakon hadurran jiragen sama.
Kwamishina kuma babban jami’in hukumar binciken haddura ta kasa Akin Olateru, ya bayyana haka
Wannan shi ne daga shekarar 1969 zuwa 2022, lokacin da jimillar mutane 2,038 (1,996 na fasinjojin jirgin da 42 a kasa) suka yi asarar rayuka sakamakon hadurran jiragen sama.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar duniya ta 2022, yayin tunawa da wadanda hadarin jirgin sama ya rutsa da su a jiya Lahadi a Abuja.
Akin nOlateru ya ce, Ku tuna cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Iyalan wadanda hadari ya rutsa da su ta Kasa da Kasa, sun aje ranar 20 ga Fabrairu a matsayin ranar tunawa da wadanda hatsarin jirgin ya shafa da iyalansu.
Olateru ya jajantawa iyalan wadanda hatsarin jirgin ya rutsa da su, ya kuma ba su tabbacin cewa masu kula da harkokin sufurin jiragen sama,sun kuduri aniyar ganin irin wannan hatsarin bai sake faruwa ba.
Ya ci gaba da cewa, “Manufofi da ka’idojin Kungiyar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya, sun tabbatar da ganin an magance bukatun wadanda abin ya shafa da iyalansu cikin lokaci. Kamar dai yadda yake a kowane lamari na gaggawa. Yana da mahimmanci a yi shiri don tallafawa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
“ya kamata a girmama Wadanda hadarin ya shafa suka tsira tare da mutunta iyalansu su da kuma tausayawa masu.