Mummunan Hatsaarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara a Ilori

Mummunan hadarin mota da ya afku a jiya Lahadi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara a Ilorin jihar kwara.

Hatsarin motar ya afku ne a unguwar filin saukar jiragen sama na Ilorin dake kan titin Ilorin zuwa Legas da misalin karfe 8:00 na safe, ya hada da wata motar fasinja ta kasuwanci da wata motar gida.

Bayanai sun nuna cewa,daya daga cikin motocin da hatsarin ya rutsa da su na dauke da jarkokin man fetur.

Motocin sune mota kirar Toyota Corolla, mai lamba LRN 787 FE da kuma motar bas Toyota Hiace.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa mutane takwas sun tsira daga hatsarin, amma da raunuka da dama.

Majiyar hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, ta jihar Legas ta bayyana cewa, motar bas din da ta taso daga Legas, ta yi lodin ne a wurin shakatawa na Geri Alimi, inda ta doshi Ilorin, a lokacin da ta kutsa cikin motar gida da ta fito daga filin jirgin.

An tabbatar da cewa, motocin sun yi taho-mu-gama ne, abin da ya haifar da motocin suka kama da wuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *