A shirye nike in sake shigar da kara kotun koli- Shekarau

Tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC da aka fisa da G-7 Sanata (brahim Shekarau ya ce, a shirye yake ya sake mika kara zuwa kotun koli domin tabbatar da adalci.

A ranar Alhamis ne bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasara a kotun daukaka kara, inda kotun ta yi watsi da hukuncin da wata babbar kotun Abuja ta yanke, wanda ya baiwa bangaren Shekarau nasara.Yana mai cewa, babbar kotun ta yi aiki ba tare da hurumin sauraren karar da aka shigar kan zaben cikin gida na jam’iyyar APC a Kano na kananan hukumomi da na gundumomi da ‘yan majalisun tarayya suka gudanar ba.

Kotun daukaka kara ta yi fatali da hukuncin da kotun babban birnin tarayya ta yanke na amincewa da taron zabe na bangaren Shekarau da aka gudanar a shekarar da ta gabata, a kan na bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje.

Da yake mayar da martani a jiya, Shekarau ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, ya kuma ba da tabbacin cewa bangaren G-7, zai yi duk abin da ya dace cikin mutuntaka da bin doka, don tunkarar lamarin a kotun koli.

A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da kungiyar masu ruwa da tsaki ta sanya ma hannu a jiya Juma’a,ta tabbatar ma masu biyayya da magoya bayanta cewa, za a kalubalanci hukuncin kotun daukaka kara a kotun koli, saboda rashin gamsuwa da hukuncin a kotun daukaka kara.

Sanarwar da ta samu sa hannun hadin guiwar Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Barau I. Jibrin, da Tijjani Abdulkadir Jobe da Nasiru Abduwa Gabasawa da Barr. Haruna I. Dederi da Sha’aban Sharada da Alhaji Shehu Dalhgatu.

Sanarwar ta ce: “Hakika, muna girmama kotunanmu da tsarin shari’armu sosai. Kuma kowane alkali yana da ikon yanke hukunci, ko ta waca hanya, dangane da duk wani lamari da ya zo gabansa.

Wani abin burgewa, shi ne yadda tsarin daukaka kara na kotunanmu ya baiwa wanda bai gamsu da hukuncin da wata kotu ta yanke ba damar ya daukaka kara zuwa wata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *