‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 22 tare da raunata 4 a kauyen Idon

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi garkuwa da mutane 22 tare da raunata wasu hudu a jiya Laraba, a garin Idon da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Mista Aboki Danjuma mazaunin Idon, ya shaida wa majiyarmu ta DAILYPOST da yammacin Laraba cewa, ‘yan ta’addan sun zo ne da misalin karfe 12:30 na safe.

Ya ce, ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe kai-tsaye, suna karya kofofi da tagogi.

Haka kuma, wani kansila a karamar hukumar Kajuru, Bala Jonathan ya ce, bayan harin, sun gano cewa ‘yan bindigar sun tafi da mutane 22 tare da jikkata mutane 4.

Ya zuwa hada wannan rahoto, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai tabbatar da kisan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *