An yi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta dakatar sufeto janar na “yan sanda

Shahararren dan gwagwarmaya a shafukan sada zumunta kuma tsohon mai taimaka ma shugaban kasa, watau Reno Omokri, ya caccaki shugaban kasar a kan gazawar da ya yi na korar Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba.

A cewarsa, ya kamata a sallami shugaban na‘yan sanda, bayan dakatarwar  sandan,sai gas hi an ga Abba Kyari a wajen daurin auren dansa shugaban makonni biyu da suka wuce.

Idan dai ba a manta ba, tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan da ke ba da amsa ga jami’an leken asiri na rundunar ‘yan sandan farin kaya, ya halarci daurin auren Maina Alkali, dan Alkali Baba.

Wannan dai shi ne karon farko da aka ga Kyari a wani taron jama’a, tun bayan fusata da aka yi da shi a shafinsa na Facebook a ranar 4 ga watan Agusta shekarar 2021, a cikin wata takaddama da ke da alaka da zargin damfara ta yanar gizo, tsakaninsa da Hushpuppi.

Yayin da ’yan Najeriya suka kasa cimma matsaya kan alakarsa da Hushpuppi, a halin yanzu tsohon jami’in dansandan Kyari na tsare, bisa zarginsa da dangantaka da kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi.

Idan za a tuna cewa, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Tafa Balogun a Legas, duk da cewa ya yi murabus ba zato ba tsammani sakamakon zargin cin hanci da rashawa a zamanin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Omokri ya yi hakikance cewa, haka ya kamata a yi wa wadanda aka samu da wannan dabi’a a ma’aikatun gwamnati, yana mai kira ga shugaba Buhari da ya dauki kwakkwaran mataki.

“Idan da Buhari ya ji kunya, da yanzu shugaban na ‘yan sanda ya rasa aikin yi, domin karbar bakuncin Abba Kyari da aka dakatar a bikin daurin auren dansa makonni 2 da suka wuce,”a rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *