Darakta Janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Hon CID Maduabum,a jiya Laraba,ya bayyana rashin halartar shugaban kungiyar gwamnonin,kuma gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, a taron gwamonin da aka yi a Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Litinin da ta gabata.
Maduabum ya ce, rasuwar Alhaji Hassan Danbaba, Magajin Garin Sokoto kuma jikan Sardauna, tare da manyan baki da suka ziyarci Sokoto don jaje, ya sa gwamna Tambuwal ya kasa barin halifancin a lokacin taron.
Mataimakin shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Abia, Dr Okezie Ikpeazu ne ya jagoranci taron gwamnonin.
Taron wanda ya samu halartar gwamnonin da basu gaza 11 ba, ya zo daidai da cikar shekaru biyu na Sanata Duoye Diri kan karagar mulki a jihar Bayelsa.
An yi ta yada jita-jitar cewa, rashin halartar Gwamna Tambuwal a taron ba zai rasa nasaba da baraka da ake gani a tsakaninsa da wasu gwamnonin ba.
Sai dai kuma Hon. Maduabum ya yi watsi da irin wadannan zage-zage, yana mai cewa, hakan ba gaskiya ba ne.
“Babu gaskiya a cikin waɗannan zage-zagen. Kungiyar Gwamnonin PDP ba ta da karfi, kuma dangantakar da ke tsakanin mambobin na da kyau sosai. Babu rarrabuwa a cikinta. Dukkansu suna aiki tare domin kafa wani sabon tsari a Najeriya ta hanyar jam’iyyar PDP,”in ji shi.