Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, a jiya Laraba ta ce, ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda biyu da suka addabi yankin karamar hukumar Chikun a jihar.
A wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ASP Muhammad Jalige ya fitar ya ce, an kama ‘yan bindigar biyu ne bayan da wani da aka yanke masa hannu a wurin masu garkuwa da mutane, ya gano su a kauyen Sabon Gaya da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Jalige ya ci gaba da cewa, ‘yan fashin guda biyu da aka kama, suna cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo bisa tuhumar aikata laifuka a jihar.
A cewar Muhammad Jalige“An gano wadanda ake zargin ne da daya daga cikin wadanda abin ya shafa wanda masu laifin suka yanke masa hannu a lokacin da yake hannunsu a ranar 8 ga wannan wata na Fabrairu.”
Ya kara da cewa, “a ranar 15 ga wannan wata na Fabrairu, jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki a bangaren Toll Gate, tare da rundunar civilian JTF, sun yi amfani da sahihan bayanan sirri, tare da samun nasarar cafke wasu mashahuran masu garkuwa da mutane biyu wadanda ke cikin jerin sunayen da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.”
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya gano sunayen ‘yan bindigan mai suna Dini Samaila da ake kira Yellow dan shekara 15 da Musa Bature, inda ya kara da cewa,wadanda ake zargin sun amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama a kusa da hanyar Sabon Gaya daga Kaduna zuwa Abuja.
Ya ce a halin yanzu, rundunar na kokarin kwato makaman da suke aikinsu, da kokarin yadda za a kama wadanda ke da hannu a cikin su domin fuskantar hukunci.