KASASHEN DUNIYA SUN YI ALLAH WADAI DA IRAN DON RATAYE DAN ZANGA-ZANGA MOHSEN SHEKARI DA TA YI

Kasashen duniya sun yi tir da Allah wadai da gwamnatin Iran biyo bayan rataye dan zanga-zanga Mohsen Shekari da ta yi bayan wata shari’ar gaggawa da ta sami marigayin da laifi.

Shekari na cikin ‘yan zanga-zanga a Iran da su ka yi bara’a da gwamnatin kasar bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini a hannun jami’an ‘yan sanda a tsakiyar watan Satumba.

An samu Mohsen Shekari da laifin tare wani titi da kuma raunata wani jami’in tsaro da ke alaka da rundunar tsaron kasar.

Masu kare hakkin ‘yan adam sun yi gargadin cewa tun da Iran ta fara yanke hukuncin kisa kan ‘yan zanga-zanga to za ta iya cigaba kenan da rataye mutane.

Zartar da hukuncin kisa ga Shekari ya kara harzuka jama’a inda su ka la’anci gwamnatin kasar ta ‘yan shi’a karkashin Ayatollah Ali Khamnanei.

Masu zanga-zangar sun bazama titin da a ka kama Shekari su ka cigaba da zanga-zanga da nuna gwamnati ta tafi da Shekari inda ta dawo da gangar jikin sa.

An bunne gawar Shekari a makabartar Behesht-e Zahra a babban birnin kasar Tehran da kulawar jami’an tsaro da kuma ‘yan kalilan daga ‘yan uwan marigayin.

Amurka ta ce za ta hukunta Iran da laifin kashe jama’ar ta da kan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *