masarufi
Hukumar kula da albarkatun man fetur ta Najeriya (NNPC), a jiya Talata ta ce, tana raba lita biliyan daya na amintaccen man fetur da kanta ga gidajen mai daban-daban a fadin kasar.
Kamfanin na NNPC ya kuma bayyana cewa, lita biliyan 2.3 na fetur zai iso Najeriya daga nan zuwa karshen wannan wata na Fabarairu, domin a magance halin da ake ciki na karancin man tare da maido da wadatarsa a kasar.
Mista Adetunji Adeyemi, Babban Daraktan Rukunin na Downstream, NNPC ne ya bayyana hakan a jiya Talata a Abuja,a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Adeyemi ya ce, hakan zai magance lamarin tare da dawo da isashshen man,fiye da abin da kasar ta sa a gaba nan da kwanaki 30.
A wasu yankunan kasar, ana sayar da man fetur a kasuwannin bayan fage a kan farashin Naira 400-1000 kan kowace lita.
Da yake magana kan wannan batu, Adeyemi ya ce, NNPC ta fahimci matsalar karancin man fetur da ake samu a sassa da dama na kasar nan, sakamakon ganowa da kuma kebe wasu kayayyakin da aka hada da sinadarin methanol na manfetur.
“Ya zuwa yau, NNPC na da lita biliyan daya na man fetur, kuma man da ake rarrabawa a yau a gidajen mai daban-daban a kasar nan lafiyayye ne.
Hakazalika, ya yi nuni da cewa kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya, da masu gidajen man fetur da masu sayar da man fetur na Najeriya da kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriyal sun fara lodi da rarraba man a sa’o’i 24 a wasu wuraren da aka kebe.
=