Direbobin Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin man fetur

Rihoton Afrikanews

Mako guda bayan rahoton farko na gurbataccen man fetur, kamfanin mai na Najeriya, NNPC, na ci gaba da kokarin kawar da gurbataccen man daga gidajen mai a fadin kasar.

Kamfanin dai ya zargi wasu ‘yan kasuwa hudu da shigo da gurbataccen man fetur mai yawa wanda direbobi da dama ke zargi da lalata motocinsu.

Karancin man fetur ya haifar da rudani a manyan biranen Najeriya, Abuja da Legas, inda motocin da ke bias layin gidajen mai, suka kai tsawon daruruwan mita.

Rashin man fetur ya kuma haifar da hauhawar farashin sufuri ga jama’a, a garuruwa da dama.

Najeriya ce kasa mafi arzikin man fetur a Afirka, amma duk da man da take hakowa yawanin man da ake amfani da shi, sai an shigo da shi daga waje.

Matatun mai na kasar kodai basu aiki, ko kuma suna aiki kasa ga yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *