Lauyan kenya ya gurfana a gaban kotun duniya akan zargin cin hanci da rashawa

Lauyan kasar Kenya Paul Gicheru ya gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dake birnin Hague domin fuskantar tuhuma kan badakalar cin hanci da kuma tsoma baki a shari’ar da ta shafi tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kasar Kenya a shekarun 2007 da 2008.

Da yake gurfana a gaban alkalan, wanda ake tuhumar ya musanta zargin, kuma ya yi ikirarin cewa ba shi da laifi.

Ana zargin Gicheru da bada wasu makudan kudade ga shaidun kutun ta ICC, da kuma cin zarafi a shari’ar da ake yi wa mataimakin shugaban kasar William Ruto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *