An yi zanga-angar nuna adawa da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya

‘yan gudun hijirar Sudan da na kudu da hamadar Saharar Afirka, sun yi zanga-zanga a garin Zarzis na Tunusiya, a ranar Litinin,Inda suka koka a kan yadda aka mayar da su saniyar ware, tare da nuna bukatar a kwashe su da gaugawa daga kasar.

‘Yan gudun hijirar da aka ceto da yawa daga cikinsu a lokacin yunkurin tsallakawa tekun Bahar Rum, sun yi zaman dirshan a gaban hedkwatar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke garin Zarzis da ke kudancin Tunisiya.

Ahmed Abdallah Adam, wani dan gudun hijira dan kasar Sudan, ya bayyana dalilin da ya sa ya halarci anga-zangar. “Ba mu da wata matsala da ‘yan kasar ko gwamnatin Tunusiya, matsalarmu tana kan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya tilasta mana zama a nan, duk tsawon wannan lokaci, tare da bata mana shekaru na rayuwarmu. Akwai ‘yan gudun hijira da suka yi shekaru 5 ko 7 a Tunisia. Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar gaba daya, ta mayar da mu saniyar ware, tana cin zarafi, kuma tana nuna rashin ‘yan adamtaka.”

Yayin da suke rera wakoki tare da rike alluna, masu zanga-zangar sun bukaci a gaggauta kwashe su daga kasar Tunisia, inda wasu suka kamu da rashin lafiya.

Tunisiya da makwabciyarta Libya sun kasance matattarar bakin hauren da ke neman shiga Turai.

Kungiyar kare hakkin tattalin arziki da zamantakewar al’umma ta Tunisiya ta ce, a cikin kashi uku na farkon shekarar da ta gabata, jami’an tsaron gabar teku, sun kama bakin haure 19,500 da suke yunkurin tsallakawa tekun Bahar Rum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *