Kwamitin kula da lafiyar kwakwalwa na jihar Kano,zai fara gudanar da aikin wayar da kan al’umma akan illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi da cin zarafi mata da matsalolin kwakwalwa, a kananan hukumomi goma Sha shida a jihar.
Mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara akan harkokin lafiya,Dr. Fauziyya Idris Buba ce ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa akan matsalolin da suka addabi al’umma karo na uku, da aka shirya ma kungiyoyin mata a jihar Kano.