Majalisar dattawan Najeriya ta nuna damuwa kan sabon shirin babban bankin Najeriya CBN na takaita adadin kudin da daidaiku ko kamfanoni za su iya fitarwa a wuni.
A sabon tsarin dai na babban bankin shi ne mutum zai iya fitar da Naira dubu 20 ne a wuni sannan ya fitar da adadin Naira dubu 100 a mako. Kamfanoni ko cibiyoyi na iya fitar da Naira dubu 100 a wuni sai kuma dubu 500 a mako.
Sanata Phillip Aduda ya nuna tsarin sam bai dace ba don zai kawo babbar matsala a tattalin arzikin Najeriya don lokacin kaura kacokan zuwa amfani da na’ura wajen hada-hadar kudi bai yi ba.
Shi ma Sanata Gebriel Suswam ya ce ‘yan mazabar sa sun yi ta kiran sa don rashin amincewar su da sabon tsarin inda ya bukaci a bude damar tattaunawa kan batun don amfanin ‘yan kasa.
Shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan ya bukaci kwamitin bankuna da kudi ya tuntubi babban bankin don karin bayani kan tsarin da shi ma ya ke nuna dari-dari kan tasirin hakan ga jama’a.
Sanata Lawan ya ce a zaman majalisar na ranar talata mai zuwa za a wre lokaci don tabka muhawara a kan sabon tsarin.