An Shirya Taron Addu’a Domin Nemawa Shugaban Ma’aikata Na Fadar Gwamnatin Katsina Sauki A Wurin Ubangiji

Wata Kungiya mai suna Jiha ta Jiha ta ce, ta Shirya taron addu’oi na musamman domin neman sauki ga Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal, wanda ke fama da rashin lafiya.

Kungiyar wadda take a karkashin Jagorancin Alhaji Nura Attah Funtua, ta gudanar da taron addu’ar ne a cikin Birnin Katsina.

Shugaban Alarammomi na Jihar Katsina Gwani Alaramma Mustapha ne ya jagiranci addu’oin.

A lokacin taron, an gudanar da addu’oi na Musamman akan Allah SWT ya kawo sauki ga Shugaban Ma’aikatan Alhaji Muntari Lawal wanda a halin yanzu yake fama da rashin lafiya.

Da yake jawabi jim kadan bayan Kammala addu’oin, Shugaban Kungiyar Alhaji Nura Attah Funtua, yace ya zama wajibi akan su gudanar da addu’oin ga Shugaban Ma’aikatan.

Kamar yadda ya shaidawa The Fact 24, Alhaji Muntari Lawal mutum ne mai kima da son a aikata dai-dai a kowane lokaci kuma wanda baya da kyashin taimakawa al’umma.

Alhaji Nura Attah yace, Shugaban Ma’aikatan ya kasance mutum ne wanda ba zaka taba samunshi a cikin cin hakkin wani ko wasu ba.

A sabili da haka ya zamo wajibi mu nema mashi sauki a wurin Allah SWT “Cewar Alhaji Nura Attah ”

The Fact 24 ta tsinkaye shi yana mai cewa ba zasu gajiya ba wurin cigaba da addu’oin samun sauki ga Shugaban Ma’aikatan Alhaji Muntari Lawal.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *