Kotun manyan laifuka ta duniya (ICC) ta saurari daukaka karar kwamandan ‘yan tawaye na Uganda

A yau litinin ne za a saurari shari’ar daukaka karar tsohon shugaban kungiyar tawayen  Uganda Dominic Ongwen a gaban kotun daukaka kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

An yanke ma Dominic Ongwen hukunci ne a watan Mayu shekarar 2021. Shi ne kwamandan kungiyar asiri da ake kira Lord’s Resistance Army, a kasar ta Uganda. An yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari saboda laifin kisan kai da yi ma mata fyade.

Lauyoyin Ongwen dai sun gabatar da dalilai 90 na daukaka kara kan hukuncin da kuma wasu kusan 10 na adawa da hukuncin,abin da suka kira “kuskuren shari’a da gaskiya da kuma tsari” da kotun ta yi.

A cikin wata sanarwa da kotun ta ICC ta fitar, ta ce karar da aka shigar kan hukuncin, ita ce mafi girma da kotun ta taba yi.

An kafa kungiyar ta kira Lord’s Resistance Army ne ta hannun wani mai kiran kansa Joseph Kony, wanda ya kaddamar da wata zanga-zangar tawaye a arewacin Uganda ga shugaba Museveni.

Yakin da aka kwashe shekaru goma ana gwabzawa tsakanin kungiyar da hukumomi, ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Hukuncin da aka yanke wa Dominic Ongwen ya sami martani iri-iri a Uganda, a bara.

Za a gudanar da sauraren karar tasa ne bisa tsari, daga ranar 14 ga Fabrairu zuwa 18 ga Fabrairu wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *