GWAMNA FINTIRI YA CACCAKI GWAMNAN BABBAN BANKI EMEFIELE

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya caccaki gwamnan babban bankin Najeriya CBN da nuna cewa ya na son huce haushi kan ‘yan siyasa ne bayan kasa samun damar shiga takarar zabe.

Fintiri dan PDP da ke neman tazarce na karo na biyu, na magana ne a wajen kamfen din sa a yankin Hong da ke jihar ta Aadamawa.

An ga hotunan neman takarar shugaban kasa na Emefiele sun cika titin da ya bi gaban babban bankin na CBN lokacin zaben fidda gwani na APC inda wata kungiya ta saya ma sa fom din takara Naira miliyan 100 amma daga bisani ya nesanta kan sa daga takarar.

Umar Fintiri ya ce kawai Emefiele na bita-da-kulli ne ga ‘yan siyasa da kawo sabon tsari na takaita fidda kudi a wuni.

Gwamnan na Adamawa ya hakikance cewa sabon tsarin zai ta’azzara lamuran tattalin arzike don yanda a ka bijiro da shi lokaci daya maimakon a bi shi daki-daki.

Duk da Fintiri bai fito kai tsaye ya ce ‘yan adawa a ke son yi wa zagon kasa ba don su rasa kudin kamfen ko kula da akwatin zabe, tuni wasu ‘yan adawa su ka nuna fargabar shirin zai kare ne kan ‘yan hamaiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *