Nasarar jam’iyyar PDP a zaben Abuja alama ce ta komawarta karagar mulki

A ranar Lahadin da ta gabata ne, jam’iyyar PDP ta bayyana komawar ta kan karagar mulki a zaben da aka kammala na babban birnin tarayya (FCT) a matsayin alamar nasarar jam’iyyar a babban zaben shekarar 2023.

shugaban jam’iyyar PDP na kasa,Dr. Iyorchia Ayu, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kan sa, ya ce, za a sami irin nasarar da aka samu a zaben kananan hukumomin  birnin tarayya a zaben gwamnonin jihohin Osun da Ekiti.

Ku tuna cewa dan takarar jam’iyyar PDP Christopher Zakka, ya samu kuri’u 19,302, inda ya kada abokin takararsa Murtala Usman na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 13,240.

“Abin da muka samu yanzu a Abuja, da kujerar mulki, za a sake samun irinsa a jihohin Ekiti da Osun a karshen wannan shekara, inda za mu karbi ragamar mulki a jihohin a shekara mai zuwa, don samar da ingantacciyar rayuwa da wadata da tsaro s Najeriya,” inji shi.

Ayu ya kara da cewa jam’iyyar PDP ta dawo don ceto Najeriya, kuma nasarar da aka samu a Abuja “babban abin al’ajabi ne.”

Ya kara da cewa, shugabancin sa zai sa PDP ta koma ga samun nasara da sake gina Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *