Shugaba Buhari ya bukaci jawo matasa cikin hukumomin gwamnati

A jiya Juma’a ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da su tabbatar da cewa sun saka matasa masu kwarewa da gogewa a dukkan hukumomi kwamitocin gwamnatin tarayya.

Shugaban wanda ya bayar da wannan umarni a lokacin da yake karbar ’ya’yan jam’iyyarsa APC bangaren matasa. Ya ce shigar da matasa cikin harkokin mulki zai karfafa koyo da jagoranci a siyasa  da harkokin gwamnati.

Musamman shugana Buhari ya bukaci ma’aikatar sakataren da ta gabatar da rahoton shigar da matasa cikin shuwagabanni da kwamitocin da har yanzu ba a kafa su ba a wata mai zuwa.

Ya kuma umurci shugaban ma’aikata Gambari, da sakataren gwamnati na tarayya Boss Mustapha da su tabbatar da yin cudanya da kungiyar matasa ta APC a kowane wata, domin samun ingantacciyar dangantaka da musayar ra’ayoyi tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *