Wani Marubuci dan kasar Uganda ya tsere bayan korafin azabtarwa

Mawallafin da ya samu lambar yabo dan kasar Uganda, Kakwenza Rukirabashaija, wanda ya zargi hukumomi da azabtar da shi a lokacin da yake tsare, ya tsere daga kasar.

Lauyansa ya tabbatar da hakan,amma ba zai bayyana inda marubucin yake ba.

An bai wa Rukirabashaija izinin barin kasar ta Uganda don jinyar raunin da ya ce ya samu a cikin watan da ya gabata yayin da yake tsare a wani wuri da ba a sani ba. Izinin barin kasar an ba da shi ne bayan kotu ta bayar da belinsa.

Sai dai kotun ta ki baiwa marubucin fasfo dinsa.

An kama marubucin Kakwenza Rukirabashaija a gidansa a ranar 28 ga watan Disamba, kuma sojoji suka kai shi wani wuri da ba a sani ba. An gallazawa marubucin kamar yadda lauyansa da matarsa ​​suka bayyana.

A ranar 17 ga watan Janairu, Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta kasar Uganda ta ziyarci marubucin, ta kuma lura da “tabon da ake iya gani da raunuka a jikinsa”.

An kama Rukirabashaija a watan Disamba da ya gabata, kuma an tuhume shi da laifin yin kalaman batanci kan shugaba Yoweri Museveni da dansa a shafin Twitter.

Ana sa ran za a fara shari’ar tasa a ranar 23 ga Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *