Uwargidan shugaba Buhari ta kai ziyarar jaje a kano

A jiya Laraba ne Uwargidan shugaban Najeriya, Hajiya A’isha Buhari ta kai ziyarar jaje ga gwamnatin jihar Kano a kan rasuwar Sheikh Ahmed Bamba da  kuma iyayen yarinyar nan ‘yar shekara biyar Hanifa Abubakar, wadda malaminta kuma shugaban Makarantar ‘Noble Kids’ Abdulmalik Tanko ya kashe ta,ya kuma binne ta a harabar makarantar.

Uwargidan shugaban kasar, ta shaida ma manema labarai a fadar gwamnatin cewa, ta zo Kano ne domin gabatar da ta’aziyya ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da  mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da iyayen marigayi Hanifa bisa rasshinta haka kwatsam.

Ta ce, “A matsayinta na uwa mai ‘ya’ya a makarantun reno da na firamare, abin damuwa ne a ce malamin da aka ba amanar yara, kwatsam ya mayar da kan sa mai garkuwa da mutane, sannan ya kashe yaron da aka damka a hannunsa. Wannan lamarin ya nuna karara girman lalacewar zamantakewa a cikin al’ummarmu.”

Uwargidan shugaban kasar ta bukaci gwamna Ganduje da ya gaggauta yin aiki, tare da tabbatar da an yi adalci ta hanyar tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda aka samu da hannu cikin lamarin yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *