‘Yan sanda sun gano sassan jikin mutane a wani gadan da ba a kamala ba a Oyo

Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo, ta gano sassan jikin mutane a wani gini da ba a kammala ba a cikin wata unguwa a garin Oyo, inda ake zargin wasu masu tsafi ne suka jefar.

An jiyo cewa, wadanda ke zaune kusa da ginin da ke kan hanyar Oyo-Ilora, a karamar hukumar Oyo ta Yamma a jihar, sun fara korafi akan dazuzzuka wajen bayan sun jin wani wari.

An ce, wasu sun yi karo da sassan jikin ɗan adam ne a cikin ginin da ba a kammala ba.

An kai batun gano lamarin ne a ofishin ‘yan sanda na Oyo ta Yamma.

Wani mazaunin garin da aka bayyana sunansa da Lanre, ya shaida wa manema labarai cewa, yana nan a lokacin da tawagar ‘yan sanda suka ziyarci ginin, inda ya kara da cewa, an yi awon gaba wasu da ake zargi.

Ya ce, “Kwanaki uku da suka wuce, wani wari ne ya rika tashi daga wani gini da ba a kammala ba, kuma mazauna wurin sun yi zaton wasu na yin bahaya a wurin. Amma da suka yi bincike a yankin, an samu cikakken hannun mutum da wasu abubuwa da ke nuni da cewa akwai yiwuwar an kashe wasu a can.

“An kai koke ga‘yan sanda a Oyo, kuma sun zo sun kama wasu da ake zargi. Abin ya dame mu shi ne ’yan sandan da suka zo, ba su ba mu damar daukar hotunan sassan jikin mutane da aka gano a wurin ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *