An daure dan jarida kwanaki 14 a gidan yari a kasar Ghana

Kotu a kasar Ghana,ta daure wani dan jarida na tsawon kwanaki goma sha hudu bayan da aka same shi da laifin raina kotu a ranar Talata da ta gabata.

An kama wakilin gidan rediyon Power FM na Accra, Oheneba Boamah Bennie, a faifan bidiyo yana zargin cewa, shugaban Ghana Nana Akufo Addo, ya gana da wasu alkalai takwas, ciki har da alkalin alkalai Kwasi Anin Yeboah, bayan zaben dubu biyu da ashirin, don yin tasiri ga hukuncin kotu bayan zaben. ‘Yan adawa sun shigar da kara a kotun koli.

Kotun da mai shari’a Elfreda Dankyi, ta ci dan jaridar mai shekaru 36 tarar dala 468 ta Amirica watau Cidi 3,000 na kasar Ghana.

Babban Lauyan kasar, Godfred Yeboah Dame, wanda ya jagoranci masu gabatar da kara, ya bayar da hujjar cewa, ya kamata a hukunta wanda ya aikata laifin domin a hana wasu yin irin wadannan furuci marar tushe.

Oheneba zai yi zaman gidan yari a Nsawam.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun bayar da rahoton cewa, an tuhumi dan jaridar a kan aikata laifukan cin zarafi, da ke haifar da rashin zaman lafiya tare da wallafa labaran karya da ya saba wa sashe na 207 da 208 (1) na dokar laifuffuka mai lamba 29/60.

2 thoughts on “An daure dan jarida kwanaki 14 a gidan yari a kasar Ghana

  1. Thank you a lot for sharing this with all of us you really recognize what you are talking approximately! Bookmarked. Please also discuss with my web site =). We will have a link exchange arrangement between us!

  2. Heya i am for the first time here. I came across this board and I find It really useful & it helped me out a lot. I hope to give something back and help others like you helped me.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *