Atiku Abubakar: Zaben Babban birninn tarayya zai zama na raba gardama Akan APC

Ana gab da zaben Kansilolin da za a gabatar a birnin tarayya Abuja,a ranar Asabar 12 ga Fabrairu,wannan ta 2022, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci mazauna birnin tarayyar da ‘ya’yan jam’iyyar PDP a babban birnin, da su fito kwai da kwarkwata, kuma su yi amfani da damarsu a zaben.

Atiku Abubakar,a wata sanarwa da aka raba ma manema labarai mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai Paul Ibe a jiya Talata, ya ce, ya kamata zaben Kansilolin da za a gabatar a karshen mako a babban birnin tarayya Abuja, ya zama kuri’ar raba gardama ga irin ayyukan gwamnatin jam’iyyar APC mai iko a kasar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya lura cewa, mutanen babban birnin tarayya Abuja, kasancedwarsu kusa da fadar mulki, za su iya zamowa kyakkyawan misali ga ‘yan Najeriya, game da gwamnati mai ci a yanzu.Saboda haka, ya kamata su yi amfani da “katin zabensu don nuna ma gwamnatin APC abinda ta aikata na kuncin rayuwa ga talaka.”

“Ya kamata a zayyana ayyukan da aka yi tsakanin gwamnatocin PDP da APC su zamo jagora kan yadda al’ummar babban birnin tarayya Abuja za su kada kuri’a a ranar Asabar. Ina sa ran kowane dan jam’iyyar PDP zai yi alfahari da jam’iyyar a wannan zabe, har ma da hada kan iyalai da aboka domin kada kuri’a da zaben ‘yan takarar jam’iyyar PDP a dukkanin kananan hukumomin babban birnin tarayyar a ranar Asabar,” in ji Atiku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *