Osinbajo ba zai tsaya takara a zaben shekarar 2023 ba – Daniel Bwala

Daniel Bwala jigo a jam’iyyar APC, ya bayyana cewa, mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ba zai tsaya takarar neman shugaban kasar ba a szaben da ke tafe na shekarar.

Bwala ya bayyana cewa, tsawar Osinbajo takara Shugaban kasa, zata zama illa gare shi, tunda shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya nuna sha’awar tsayawa takarar.

Rahotanni a ranar Litinin da ta gabata, sun bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar Osinbajo, zai bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa, bayan babban taron jam’iyya mai mulki da aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Fabrairu, 2021.

Amma, mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ya yi watsi da irin wadannan maganganu, wanda ya bayyana a matsayin karya da hasashe.

Bwala ya jaddada cewa sabanin irin wadannan rahotanni, mataimakin shugaban kasar ya yi watsi da irin wannan yunkuri.

“Ina jin na san hikimar da ke tattare da dalilin da ya sa mataimakin shugaban Osinbajo, ba zai yi takarar ba, kuma yana watsi da duk wani yunƙuri na nuna hakan” in ji Bwala.

Ya kuma bukaci Osinbajo da ya fito fili ya musanta rade-radin da ake yi na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Ya kuma yi kira ga mataimakin shugaban kasa da ya fito fili ya goyi bayan aniyar Tinubu ta neman shugaban kasa.

A kwanakin baya ne Tinubu ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar neman kujera mafi girma a Najeriya a siyasance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *