Majalisar Dattawa ta Najeriya ta amince da Sabbin cibiyoyin koyon aikin lauya

Majalisar dattawa ta Najeriya amince da kafa sabbin cibiyoyi shida na makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya a shiyyoyin shida na siyasa a kasar nan.

Sabbin makarantun da aka amince da su, kari da bakwai da ake da su, sun kawo adadin makarantun shari’a a kasar zuwa sha ukku, ban da ta babban birnin tarayya Abuja.

Amincewa da sabbin makarantun shari’ar, ya biyo bayan la’akari da rahoton da Ma’aikatar Shari’a da ‘Yancin Dan Adam da kuma al’amuran Shari’a ta yi kan duba kudirin dokar ilimin Shari’a na shekarar 2021.

Sanata Smart Adeyemi daga mazabar  Kogi ta Yamma ne ya gabatar da kudirin dokar.

saboda haka, Majalisar ta dattawa ta amince da makarantar koyon aikin lauya ta Jos a jihar Filato. Da Makarantar Lauyoyi ta Kabba dake Jihar Kogi.

Majalisar ta kuma ba da takardar amincewa ga makarantar koyon aikin lauya ta Yola a jihar Adamawa da kuma da makarantar koyon aikin lauya ta Maiduguri a jihar Borno.

Haka kuma, Majalisar Dattawan ta amince da makarantar koyon aikin lauya ta Kano dake jihar Kano,sai sai makarantar koyon aikin lauya dake  Argungun Jihar Kebbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *