Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’in kula da ababen hawa a jihar Anambara

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a garin Ekwulobia da ke karamar hukumar Aguata a jihar Anambra, tare da kashe jami’an kula da ababen hawa da safiyar yau Talata.

Wani ganau ya shaidawa DAILY POST cewa, kawo yanzu ba a bayyana ko mutanen ’yan fashi da makami ne, ko ’yan daba ko kuma ’yan bindiga.

Majiyar ta ce, an harbe wani ma’aikacin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Anambra da ba a tantance ko wanene ba,a lokacin da yake kula da cunkoson ababen hawa a mahadar ta Ekwulobia, inda harsashi ya farfasa kansa daga baya.

Ba a sami jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *