Jami’an kashe gobara sun kashe wutar da ta kwashe kwana biyu tana barna a kasar Kenya

Jami’an kashe gobara a kasar Kenya sun sami nasarar kashe wata gobara da ta kwashe kwanaki biyu tana barna a dajin Aberdare na kasar Kenya, bayan da ta kone dajin da ya kai kadada dari, in ji wani jami’in kula da gandun daji na gwamnati jiya Litinin.

Gobarar dai ta tashi ne a ranar Asabar din da ta gabata, kuma masu kula da gandun daji da dama, da masu kashe gobara da kuma masu aikin sa kai sun yi ta kokarin dakile yaduwa wutar.

Shugaban hukumar kula da gandun daji ta Kenya Samuel Ihure, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an dakile gobarar gaba daya, inda ya kara da cewa kusan hekta 600 na daji ta kone.

Wata kungiyar ba da agaji ta ‘Rhino Ark’ a kasar Kenya, a baya ta ce ta aike da jirage masu saukar ungulu don gudanar da binciken sararin samaniyar yankin domin tantance girman barnar da ta afku a gandun daji.

“Ma’aikatan kashe gobara 35 ne aka tura su a ofishin kashe gobara na kudanci,” in ji kungiyar a bayanin da ta wallafa a shafin Twitter a jiya Litinin.

“Muna da ma’aikatan kashe gobara wadanda ke yin aiki a can. Ya zuwa yanzu, sun sami nasarar shawo kan gobarar, amma ba a kammala ba,” in ji jami’in Rhino Ark Adam Mwangi.

Jami’in ya yi zargin cewa, go barar tana faruwa ne sakamakon ayyukan da jama’a ke gudanarwa a dajin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *