Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun dakatar da shirin yajin aiki a fadin kasar nan

Kungiyoyin ma’aikatar kamfanin zirga-zirgar jiragen sama, sun dakatar da wani shirin yajin aikin da suka shirya yi a ranar yau takwas ga wannan wata na Fabrairu a faɗin ƙasar nan.

Ministan Kwadago Sanata Chris Ngige ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen wani taron sasantawa da aka yi a safiyar yau Talata a Abuja.

Ma’aikatar jiragen karkashin kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta kasa (NUATE), da kungiyar kwararrun ma’aikatan sufurin jiragen sama (ANAP), sun yi barazanar kaurabe ma ayyukansu a wannan ranar takwas ga watan Fabrairu, saboda kasa samar da jin dadin ma’aikata, da kuma kasa aiwatar da  yarjejeniyoyin da suka kulla da gwamnati.

Ngige ya ce, bukatu biyu na kungiyoyin, sun hada da rashin aiwatar da mafi karancin albashin ma’aikata a cikin Ma’aikatar, tun shekarar 2019, da kuma rashin amincewa da sharuddan aiki da aka duba a cikin ma’aikatun.

Ya ce an cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin ma’aikatan da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya.

Ngige ya ce, an cimma matsaya a kan wasu kudurori ne bayan kammala tattaunawa kan batutuwan da bangarorin suka amince da su.

“An bukaci Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kasa (NSIWC), da ta fitar da wata takardar yarjejeniyar aiki da ta sanar da dukkanin bangarorin gwamnati da masu zaman kansu cewa, su daure su aiwatar da mafi karancin albashi na kasa na shekarar 2019.

“Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama za ta raba daftarin aiki, a kan yadda ya kamata a daidaita mafi karancin albashi ga dukkan hukumomin da ke karkashin kulawar ma’aikatar.

Ya kuma bukaci su aiwatar da tsarin mafi karancin albashi na kasa, ba tare da wani bata lokaci ba, sannan su tabbatar cewa, wannan biyan ya fara aiki ne daga ranar sha takwas (18) ga watan Afrilu, 2019,wanda shi ne lokacin da aka sanya hannu a kan mafi karancin albashin ma’aikata,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *