Babbar kotun tarayya dake Kano ta dage zaman sauraron  shari’ar Mahdi shehu da Ofishin Sufeton ‘yansanda na Najeriya

Babbar Kotun Tarayya dake  Kano, ta dage zaman Sauraren Shari’a Tsakanin Ofishin Sufeton ‘Ƴansanda  da Mahadi Shehu zuwa ranar ashirin da takwas ga watan Fabrairu da kuma ranar daya ga watan Maris mai zuwa.

Hakan zai bada dama ga ɓangaren masu ƙara su kawo sahihan takardu, da kuma gabatar da wasu ƙarin shedu a gaban kotun, domin kare kansu dangane da batun zarginsu da ake yi da sama da faɗi da dukiyar al’ummar jihar Katsina.
A yayin zaman kotun da aka fara da misalin ƙarfe uku na ranar Litinin, wanda mai Shari’a Abdullahi Liman ya jagoranta, bangaren lauyoyi masu tuhuma ya tambayi ɗaya daga cikin shedun gwamnatin jihar Katsina, kuma Sakataren Gwamnatin jihar, Dr. Mustapha Muhammad Inuwa kan abinda ya sani dangane da zargin da ake ma gwamnatin.
A jawabinsa, Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, bayan ya yi rantsuwa da Allah cewa duk abinda zai faɗa gaskiya ne, ya ƙaryata duk zargin da ake ma gwamnatin jihar bisa yin sama da faɗi da dukiyar al’umma.
Ya ƙara da cewa an yi hakane kawai don a ci mutuncin Gwamna da wasu daga cikin muƙarrabansa, tare da cusa ƙiyayya da gaba a cikin zukatan masoyansu.
Ya ce, a sanadiyar zargin da ake ma gwamnatin, da yawa daga cikin al’ummar jihar mazauna ƙasashen waje da sauran wurare, sun sha kiran gwamnatin inda suke nuna rashin jin daɗinsu dangane da al’amarin.
Ya ƙara da cewa iyalansu, su ma ba a barsu a baya ba a makarantunsu wajen nuna masu tsangwama wanda da yawansu sun baro makarantun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *