MAJALISAR WAKILAI TA SAKE AMINCEWA DA DOKAR KAFA RUNDUNAR ZAMAN LAFIYA

Majalisar wakilan Najeriya ta yi zama da sake amincewa da kudurin dokar kafa rundunar zaman lafiya watp PEACE CORPS.

Dan majalisa Muhammad Monguno ne ya gabatar da kudurin inda majalisar ta bi duk sassan kudurin inda ta amince da kafa rundunar.

Dama majalisar dattawa ta amince da kudrin yayin da Sanata Muhammad Ali Ndume ya gabatar da kudurin.

In za a tuna majalisa ta 8 karkashin Sanata Bukola Saraki ta amince da kudurin kafa rundunar inda amincewa da ita daga shugaba Buhari ya samu cikas bisa karancin kudi da gujewa kafa rundunoni masu aiki iri daya.

Yanzu ya nuna za a mayar da kudurin wajen shugaba Buhari don yiwuwar samun amincewa don fara aikin rundunar da ta ke samun matukar tsama daga rundunar ‘yan sanda.

Kwamandan rundunar Dickson Akoh ya ce sabon kudurin ya magance duk dalilan da su ka saka shugaban kasa bai amince da rundunar a baya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *