
Jam’iyyar APC mai mulki, ta lashe dukkan kujerun kananan hukumomi ashirin da daya da kansilolin jihar Kebbi.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kebbi Aliyu Muhammad Mera, wadda aka rabawa manema labarai ta ce, sakamakon zaben ya zo daidai da yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomin. wanda aka gudanar a ranar 5 ga watan Fabrairun wannan shekara.
Sanarwar ta ce, bisa la’akari da sashe na 179 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999, wanda ya bai wa hukumar dammar tsarawa da sa ido, da kuma gudanar da zabukan kananan hukumomin jihar, da aka gudanar a kananan hukumomi ashirin da daya, da yankunan da kuma unguwanni dari biyu da ashirin da biyar a jihar.
Sai dai sanarwar ta yaba da gudumawar da masu ruwa da tsaki kamar kafafen yada labarai da tsaro, da kungiyoyin farar hula da musamman jam’iyyun siyasa ke bayarwa.