Babban  hafsan Sojoji ya umurci kwamandojin tsara bata-kashi da su dauki matakan magance rashin tsaro a Najeriya.

 Babban Hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya umarci kwamandojin rundunar da su yi amfani da dabaru da daukar matakan da suka dace   gami da kwarin gwuiwa don magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane, a yankunan da suke aiki. Ya ba da wannan umarni ne a jihar Minna ta jihar Neja, a ci gaba da tantancewa da sake duba ayyukan sojojin da ke yaki da miyagun laifuka a Najeriya.

 Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce, dole ne sojojin su yi taka-tsan-tsan, tare da bin diddigin yadda za a kawar da duk wasu kurakurani na aiki, a yakin da ake yi da ‘yan fashi da makami. Zai kuma so kada su yi kasa a gwiwa wajen isar da kalubalen nasu ga shugabannin Sojoji, domin daukar matakin da ya dace. Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya kuma umarce su da su yi aiki tare da sauran jami’an tsaro, don wargaza hanyoyin sadarwar ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka a yankunansu yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *