MUN GANO KIMANIN NAIRA TIRILYAN 4 DA A KA KARKATAR DAGA BINCIKEN DA MU KA GUDANAR-GUDAJI KAZAURE

Dan majalisar wakilai Muhammad Gudaji Kazaure ya ce wani kwamitin da shugaba Buhari ya nada su na bincike a lamuran hada-hadar kudi a babban banki, ya gano karkatar da kudi kimanin Naira tirilyan 4.

Kazaure ya ce an kafa kwamitin na su cikin sirri kuma an nada su, su 7 su yi aikin binciken kuma shi ne sakataren kwamitin.

Dan majalisar ya kara da cewa ya na da cikakkun bayanna da ya ke son gabatarwa kan wannan binciken don jama’a su san halin da a ke ciki.

Kazaure ya ce zai yi bayanai filla-filla kan dalilan da ya sa a ka sauya fasalin kudi da kuma yanda za a iya samun kudin ciyar da kasafi ba tare da ciwo bashi ba.

A alhamis din nan Kazaure ke shirin ganawa da manema labaru don fitar da bayanan da ya ce ya wallafa su kan takarda don kowa ya karanta ko da kuwa akwai masu zagon kasa wajen hana bayanan fitowa duniya ta sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *