Masu ikrarin kafa kasar addini a Maiduguri sun yi garkuwa da mutane

Kungiyar masu ikrarin kafa kasar addini(ISWAP) ta yi garkuwa da mutane 3 a kauyen Mandaragirau da ke jihar Borno

Rahotanni daga Kauyen da ke kudancin Borno na nuni da cewa mayakan na ISWAP sun yi awon gaba da mutane uku da sanyin safiyar yau Asabar.

An bayyana sunayen matasan ukun da aka sace,da Yamta Usman da Hamidu Adamu Chiroma da kuma Mustapha Adamu Chiroma da aka fi sani da Lingi.

Majiyoyi sun shaida ma majiyarmu cewa, “Mun wayi gari da wannan abin mamakin. Lokaci na karshe da makamancin wannan lamari ya faru a nan shi ne, lokacin da suka je kasuwa suka dauko wani. Sai dai wancan, mun samu labarin cewa suna zargin shi ne da yi ma sojoji liken asiri.”

“Ga waɗannan samarin kuwa, muna zargin cewa kungiyar ta ISWAP za ta iya amfani da su, su tura su wajen aikinsu. Kwanan nankungiyar na daukar samari daga kauyukan da ke kudancin Borno aiki.”in ji majiyarmu.

Wani mazaunin garin ya shaidawa jaridar ‘DAILY POST’ cewa abin mamaki ne ganin irin wadannan abubuwan da ke faruwa, a lokacin da labari ke nuni da cewa, sojoji na tunkarar mayakan mayakan ISWAP.

“Idan irin wannan abu zai ci gaba da faruwa ta fuskar labarai da alkawuran da ke ci gaba da faruwa, to ba mu san wanda za mu amince da shi ba. Na yi baƙin ciki da samun saƙo da sassafe cewa, kungiyar ta ISWAP ta zo ƙauyenmu ta tafi da wasu samari.

“Wannan abin bakin ciki ne. Ba mu samu labarin dalilin da ya sa aka dauke su ba. Muna addu’ar Allah ya dawo dasu lafiya. Amma ni ma ina jin tsoron faruwar lamarin musamman a kwanakin nan da irin rahotannin sace-sacen da kungiyar ke yi a halin yanzu. ” Yace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *