Kasar Iran ta bukaci makwabtanta da su gudanar da ayyukan yaki da miyagun kwayoyi

Kasar Iran ta yi kira ga makwabtan gabashin kasar, da su gudanar da ayyukan yaki da safarar miyagun kwayoyi

Manjo Janar Yahya Rahim Safavi, babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Jagoran juyin juya hali na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana a yau Asabar cewa, Iran na sahun gaba wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi a duniya, ya kuma bukaci kasashen gabashin kasar da ke makwabtaka da kasarsu, da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu don dakile wannan dabi’a.

Har ila yau babban mai ba da shawara kan harkokin soji na Jagoran, ya yi kira ga ofishin Majalisar dinkin duniya, mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuka da ya taimaka wajen kawar da takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Iran, inda takunkumin ke kawo cikas ga yaki da miyagun kwayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *