KYASHIN DUKIYA KAWAI ABOKAN HAMAIYA KE YI-TINUBU

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa Bola Ahmed Tinubu ya ce abokan hamaiyar san a kyashin dukiyar da Allah ya ba shi ne ya sa su ka caccakar sa.

Tinubu wanda ya ce gidan CHATTAM a London na zantawa ne da kafar labarun Burtaniya.

Dan takarar ya ce ai ya gaji tarin gidaje kuma ya na da hannayen jarin kasuwanci da ke kawo ma sa rina don haka masu magana a kan dukiyar san a yin kyashi da arziki ne.

Hakanan Tinubu ya ce shi ne gwamnan da a ka fi yin bincike a kan sa amma ba a gano komai ba kuma tun da ya bar mulki a 2007 bai sake karbar mukamin gwamnati ba.

Da a ka tambaye shi kan cewa ko ya na karbar sashen kudin shigar da jihar Lagos ke samarwa, Tinubu ya ce ai hukumar lamuni ta duniya ta bincika jihar Lagos, ya na mai cewa sam labarin ba gaskiya ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *