Afirka ta Kudu ta ƙirƙiri samfurin rigakafin Corona na Moderna

A yuukurin kawo karshen karancin allurar rigakafi a kasashe masu tasowa, Masana kimiyya a Afirka ta Kudu, sun yi nasarar kirkirar kwafin maganin rigakafin samfurin Moderna Covid.

Kamfanin fasahar kere-kere da ke Cape Town watau ‘Afrigen Biologics and Vaccines’ ne ya sanar da wannan ci gaban.

“Saboda haka manufar ita ce a samu wani abu mai inganci, amma samfurin maganin zai samar da kwanciyar hankali.” in ji , Manajan daraktan kanfanin Afrigen, Petro Terblanche.

Kamfanin yana aiki don sake samarda allurar rigakafin a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO) na samar da fasaha da ke da alaƙa da cutar Corona a cikin duniya.

Nahiyar Afirka ita ce nahiyar da ta fi kowace Nahiya yawan aiwatar da allurar rigakafi a duniya, inda kasashe ke dogara ga gudummawar da kasashe masu arziki ke bayarwa;wannan ya haifar da kiraye-kirayen a yi allurar rigakafin ta Corona a Nahiyar, don kawo karshen abin da masu fafutuka suka kira da allurar wariyar launin fata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *