BABBAN BANKIN NAJERIYA YA KAIYADE ADADIN FIDDA KUDI A MAKO

Babban bankin Najeriya ya fitar da sabon tsarin fitar da kudi a bankuna a duk mako inda mutum shi kadai zai iya fitar da Naira dubu 100 ne a mako yayin da kamfani ke da hururumin fitar da Naira dubu 500 a mako.

Sabon tsarin na zuwa ne a didai lokacin da bankin ke shirin sakar sabbin kudi da a ka sauyawa fasali daga tsakiyar watan nan na disamba.

Wannan ya nuna duk kudin da su ka haura wannan adadi to ya zama wajibi a biya harajin kashi 5% da kashi 10% ga daidaiku da kamfanoni.

Hakanan a na’urar ATM mutum zai iya fitar da Naira dubu 20 ne a wuni kuma an kafa dokar daga takardar Naira 200 zuwa kasa ne kadai za a dura a na’urar.

Babban bankin ya ba wa mutane shawarar amfani da na’urorin tura kudin a yanar gizo don gudanar da hada-hadar su ta kudi ba tare da lalle rike takardiun kudin ba.

Tuni wasu su ka fara dari-darin wannan tsarin ba mamaki ya zama wasu matakai ne na takura samun kudi ga ‘yan siyasar hamaiya a zaben 2023.

Sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 9 ga watan janaiu mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *