
Shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya bayyana cewa, zaman lafiya ya dawo a kasar bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a jiya Talata.
Shugaban ya sheda ma manema labarai bayan ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa, an shawo kan lamarin.
Hukumomin ba su bayar da bayanai game da wadanda harin ya rutsa da su ba ko kuma wadanda ke da hannu wajen kai harin.
A jiya Talata, an shafe sa’o’i da dama ana kai hari a fadar gwamnati yayin da shugaban kasa da firaminista ke ciki.