Mutane  Ashirin da shida sun rasa rayukansu  sakamkon katsowar  wayan lantarki

Kimanin mutane Ashirin da shida ne  suka rasa rayukansu a yau Laraba, sakamkon fadowar wayar lantarki a cikin kasuwa da ambaliyar ruwa ta mamaye a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar  Demokradiyyar Kongo, a cewar hukumomi a yankin.

Kakakin gwamnatin lardin Kinshasa, Charles Mbutamuntu, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa,babbar wayar da ke dauke da wutar ta tsinke, inda wai bangaren wayar ya fada cikin wani rami da ya cika da ruwa bayan daukewarb ruwan sama da safiyar yau Laraba.

Ramin ya ratsa cikin shahararriyar kasuwar abinci ta Matadi-Kibala da ke yammacin birnin, babban birni mai yawan mutane sama da miliyan 10.

“Yawancin mutanen da suka rayukansu ‘yan kasuwa ne da abokan cinikayya, da kuma wasu masu wucewa, an kai gawarwakin zuwa dakin ajiyar gawa, kuma an fara bincike don tabbatar daukar dawainiyarsu” in ji Mbutamuntu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *