JAM’IYYUN ADAWA SUN YI TARON KIN AMINCEWA DA SAKAMAKON ZABE

Manyan jam’iyyun hamaiyar Najeriya sun taro na musamman inda su ka aiyana rashin amincewar su da sakamakon zaben shugaban kasa da a ka gudanar ranar asabar din makon jiya.

Jam’iyyun sun bukaci a soke zaben da nuna tamkar an kwari ‘yan kasa kan dawaniyar kada kuri’a ba tare da samun biyan bukata ba.

Taron ya gudana ne gabanin aiyana sakamakon zaben da dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu ya baiyana a matsayin wanda ya lashe.

Duk da jam’iyyun kai tsaye ba su fadi abun da za su yi ba in ba a soke zaben ba, amma da alamu za su kalubalanci sakamakon a kotu.

Kan gaba a jam’iyyun akwai babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma Leba ta kungiyar kwadago wadanda har ila yau su ke kan gaba a samun kuri’a bayan jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *