A karo na farko cikin shekaru 6, babban sakataren majalisar dinkin duniya sauka a birnin Bagadaza na kasar Iraki don ziyarar aiki ta musamman.
Babban sakataren Aantonio Guterres ya ce ya ziyarci Iraki ne don karfafa guiwar al’ummar kasar da su ka sha faman fitina inda yanzu dimokradiyya ta kara zama bayan samun tsaiko na rashin jituwa.
Guterres wanda ya sauka a daren talata zai gana da firaministan Iraki Muhammad Shia Alsudani a yau larabar nan.
Kazalika sakataren kamar yanda yanayin aikin majalisar dinkin duniya ya ke zai yi taro da kungiyoyin mata da matasa.