BOLA TINUBU YA LASHE ZABEN SHUGABAN NAJERIYA

Dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben shugaban Najeriya da a ka fafata tsakanin jam’iyyu 18.

Tinubun dai ya lashe ne don yawan kuri’a amma sauran abokan takarar ta sa Atiku na PDP da Peter Obi na Leba sun samu kashi 25 na yawan kuri’a a 2/3 na yawan jihohin Najeriya.

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ke aiyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da sama kuri’a miliyan 8.8 inda ya dara mabiyin sa a yawan kuri’a Atiku Abubakar da ke da sama da kuri’a kuri’a miliyan 6.9.

Peter Obi na jam’iyyar Leba ke zama na uku da yawan kuri’a sama da miliayn 6.

Wani abun dace duk manyan ‘yan takarar uku sun yi galabar a yawan kuri’a a jihohi 12 kowanne inda Rabi’u Kwankwaso na NNPP ke zama na hudu da galabar a jihar Kano.

Bai zama abun mamaki ba a ce Tiunbu ya yi nasara a jihohin yarbawa, ko Atiku ya samu nasarar da ya sake samu yanzu, amma yanda Peter Obi ya girgiza zaben da samun mara baya a jihohin kudu maso gabar da kudu maso kudu da lashe jihar sa da gagrumin rinjaye duk da rashin jituwar sa da gwamna Charles Soludo ya zama abun mamaki ko darashin tattaunawa.

Tuni ‘yan APC su ka hargitse da murnar samun wannan nasara da nuna kwarin guiwar shugaban mai jiran gado ba zai nuna bambanci a mulkin sa tsakanin dukkan sassan Najeriya ba.

Gabanin nan, manyan jam’iyyun adawa da su ka hada da PDP da Leba sun yi watsi da sakamakon da bukatar a soke zaben.

Za a jira a ga yanda lamura za su cigaba da kasancewa har zuwa ranar 29 ga watan mayu yayin da shugaba Buhari zai sauka daga mulki a rantsar da sabon shugaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *