EMEFIELE YA YI KEMEME YA KI AMINCEWA DA UMURNIN KOTUN KOLI

Shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya yi kememe ya ki amincewa da umurnin kotun koli na cigaba da amfani da tsoffin kudi har sai an kammala sauraron karar da jihohi 3 su ka shigar.

In za a tuna jihar Kaduna, Kogi da Zamfara sun hada kai su ka kai karar dakatar da babban bankin daga tsayar da amfani da tsoffin kudi daga ranar 10 ga watan nan da ta wuce.

A ziyarar da ya kai ma’aikatar lamuran kasashen waje, Emefiele ya ce ba wani dalilin kara wa’adin daga ranar 10 ga wata don an dau duk matakan da su ka hada da iya karbar kudi a kan kantar bankuna don saukakawa mutane damar samun kudin.

Gwamnan ya kara da cewa za a cafke duk wani mai na’urar POS da ke cajin fiye da Naira 200 kan fitar da kudi matukar a ka kama shi da laifin.

Alamu na nuna babban bankin da ke da goyon bayan shugaba Buhari na neman biris da umurnin babban bankin tamkar ba a ba da wani umurni ba.

Alamu na nuna burin da a ke neman cimmawa kafin ganin sauki sai bayan kammala babban zaben nan na ranar 25 ga watan nan.

Za a jira a ga fara shari’ar da kotun kolin za ta yi a larabar nan ko za a dau sabon mataki ko kuwa a’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *