A wannan Talata ne aka rika jin karar harbe-harben bindigogi a babban birnin Guinea Bissau.
Rahotannin daga kasar sun bayyana cewa, wasu mutane dauke da makamai sun zagaye fadar shugaban kasa.
Ana kyautata zaton shugaban kasar Umaro Dissoco Embalo, da Firaminista Nuno Gomes Nabiam suna wajen taron majalisar ministocin kasar.
Fadar gwamnatin Guinea Bissau tana kusa da filin saukar jiragen sama na kasar.
maharan na tsare da wasu jami’an gwamnatin kasar