MDD TA NUNA FARIN CIKI GA AMINCEWA DA BUDE HANYOYI BIYU DON ISAR DA AGAJI GA AREWACIN SHAM

Babbar sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya nuna farin ciki amincewar da shugaban Sham Bashar Al’Asad ya yi na bude wasu mashigu biyu daga Turkiyya don isar da kayan agaji yankin arewa maso yammacin Sham da ke hannun ‘yan hamaiya.

Mashigun biyu daga Turkiyya sun hada da Babal Salam da kuma Al-ra’ee da za su yi matukar taimakawa wajen saukaka shigar da kayan tallafin da dimbin mutanen da girgizar kasa ta raba da matsugunan su.

Majalisar dinkin duniyar ta ce Bashar Al’Asad ya amince da bude hanyoyin a karon farko na tsawon wata 3.

Tsanantar rasa rayuka a sanadiyyar girgizar kasar ya jawo daukar matakin don a kasashen biyu na Sham da Turkiyya fiye da mutum dubu 33 su ka mutu.

A sham kadai mutum dubu 4,300 su ka mutu inda dubu 7,600 su ka samu raunuka kuma a na ganin za a kara samun asarar rayuka don har yanzu akwai mutanen da ke karkashin gine-gine da ba a gano ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *