AN SAKE BANKAWA WANI OFISHIN HUKUMAR ZABE WUTA A JIHAR IMO

A cikin hare-hare kan cibiyoyi da jami’an gwamnatin taraiya a yankin kudu maso gabar, an bankawa wani ofishin hukumar zabe wuta.

Hukumar zaben INEC a takaice ta ce maharani sun cinna wuta ga ofishin ta da ke yankin karamar hukumar Oru ta yamma.

INEC ta ce lamarin ya shafi dakin taro ne inda kujeru su ka kone amma an yi sa’a bai shafi muhimman kayan aiki ba.

A dan tsakanin nan ma ko farkon watan nan an kai hari kan ofishin hukumar a yankin karamar hukumar Orlu a jihar ta Imo.

An aza alhakin irin wadannan hare-hare kan kungiyar ‘yan aware na Biyara ta IPOB da shugaban ta Nnamdi Kanu ke fuskantar shari’ar ta’addanci da cin amanar kasa a gaban babbar kotun taraiya da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *