TUNI HAR PDP TA JERA SUNAN YAKUBU DOGARA A CIKIN MEMBOBIN KAMFEN DIN SHUGABAN KASA

Tuni har babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP ta jera sunan tsohon kakakin majalisar dokokin Najeriya Yakubu Dogara ajerin ‘yan kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Wannan ya faru ne bayan bangaren kungiyar mabiya addinin kirista na arewa da Dogara ke jagorantar ta aiyana mara baya ga dan takarar jam’iyyar.

Sanarwar nadin Dogara ta fito ne daga shugaban kamfen din PDP Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal.

In za a tuna Dogara da wasu manyan mabiya addinin kirista a arewa sun ki amincewa da dan takarar jam’iyyar APC don cankar musulmi Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin takara.

Za a jira a ga irin tasirin da matakin zai dauka a kamfen din yayin da jigon kungiyar kiristocin Babachir Lawal a wata hira shi kuma ya mika wuya gad an takarar jam’iyyar Leba Peter Obi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *